Tevez ya nace sai ya bar Man City

Tevez  ya nace sai ya bar Man City
Image caption Tevez ya dade yana sa'insa da mahukuntan City

Carlos Tevez ya nace sai ya bar Manchester United saboda dangantakar sa da wasu shugabannin klob din ta yi tsamin da ba za ta gyaru ba.

City ta yi watsi da bukatar da dan wasan ya gabatar a rubuce ta neman tafiya, yana mai bayyana matsalar iyali.

Ya bayyana cewa "ba shi da wata matsala" da koci Roberto Mancini.

Sai dai Tevez ya ce: "Wannan wani mataki ne da na dauka tun da dadewa kuma na shafe lokaci mai tsawo ina tunani a kai."

A wata sanarwa da ya fitar, "Tavez ya gode wa mai kungiyar Sheikh Mansour saboda goyon bayan da ya bashi".