Blackburn Rovers na zawarcin Diego Maradona

Maradona
Image caption Diego Maradona ne ya jagoranci Argentina zuwa Afrika ta kudu

Akwai alamun cewar kungiyar Blackburn Rovers na zawarcin tsohon kocin Argentina Diego Maradona da niyyar nada shi koci.

Kampanin Venky Group na Indiya me mallakar Blackburn ya kori Sam Allardyce a matsayin koci a wani yinkurin sake fasalin kungiyar, kuma yana kokarin ganawa da Maradona akan mukamin.

Masu kungiyar sun ce manufarsu itace Blackburn Rovers ta shiga cikin sawun kungiyoyi biyar na farko a teburin gasar premier.

Shugaban kamfanin Venky Anuradha Desai ya tabbatar da cewar sun fara tattaunawa da Maradona amma dai kocin riko Steve Kean shine zai cigaba da jan ragama har zuwa karshen kakar wasa ta bana.