Za a kori Grant a West Ham idan bai samu nasara a wasa ba

Grant
Image caption Grant na fuskantar matsin lamba

Za a kori kocin West Ham Avram Grant idan ya kasa samun nasara a wasa guda cikin uku masu zuwa a gasar premier ta Ingila.

Grant dai ya samu galaba ne a wasa daya cikin goma sha daya kuma a halin yanzu kungiyar ce ta karshe a teburin gasar.

Rahotanni sun nuna cewar Sam Allardyce wanda aka kora a Blackburn na daga cikin wadanda ake tunanin za a baiwa ragamar kungiyar.

West Ham a wasanta na gaba zata kara da Blackburn sannan sai fafatawa da Fulham kafin ta dauki bakuncin Everton.

Mataimakin shugaban West Ham Karren Brady ya shaidawa BBC a watan daya gabata cewar za a iya barin Grant ya cigaba da horadda 'yan West Ham har zuwa karshen kakar wasa ta bana.