An kori kocin Tunisia Bertrand Marchand

Bertrand
Image caption Watanni shida kacal Bertrand ya shafe a Tunisia

Dan kasar Faransa Bertrand Marchand ya ce yaji mamakin korarshi da hukumar kwallon Tunisia tayi.

An kori Marchand tare da sauran mataimakanshi a ranar Laraba sakamakon kasa taka rawar gani.

Dan shekaru hamsin da bakwai ya kulla yarjejeniya ta shekaru biyu da Tunisa har zuwa watan Yunin 2012 kuma an bashi alhakin jagorantar kasar zuwa gasar cin kofin kasashen Afrika a 2012.

Marchand yace"naji mamaki kuma abin kunya ne saboda akwannan muka tattauna akan makomar tawagar".

A baya da Marchand ya samu goyon bayan hukumar kwallon duk da kashin da kasar ta sha a wajen Botswana da kuma canjaras din da suka buga tsakaninsu da Malawi a wasannin share fage.

A rukunin K dai, Tunusia na bayan Botswana ce inda aka fita da maki shida.