Gyan ne zakaran kwallon Afrika na BBC a bana

Image caption Asamoah Gyan

Dan wasan kasar Ghana da kuma kungiyar Sunderland Asamoah Gyan ne ya lashe kyautar zakaran dan kwallon Afrika na BBC a bana.

Dan wasan ya lashe kyautar ne bayan ya samu fiye da rabin kuri'un da aka kada.

Asamao Gyan ya yi zarra ne a kan dan uwansa da kasar Ghana 'Dede' Ayew da 'yan kasar Ivory Coast Yaya Toure da Didier Drogba da kuma Samuel Eto'o na Kamaru.

"Ina matukkar farin ciki, ban zata zan iya lashe kyautar ba, inawa magoya bayana godiya, saboda kuri'un da su ka jefa mun."

Asamoah Gyan ya rasa ta cewa, bayan da aka shaida mishi cewar shine ya lashe kyautar.

"Abu ne mai wuya a ce mutum ya lashe wannan kyauta, ganin irin kwarrarun 'yan wasan da na yi takara da su."

"Ina kara godiya ga masoya a Afrika da kuma 'yan uwana da masoya na a Ghana."

Gyan dai ya taka rawar gani a fagen tamoula a bana, inda ya taimaka wa Ghana kaiwa matsayin ta biyu a gasar cin kofin Afrika da aka buga a Angola.

Dan wasan ya zura kwallaye uku cikin hudu da kasar ta zura a gasar, inda ta kai ga buga wasan karshe a karo na farko a tsawon shekaru 18.

A gasar cin kofin duniya da a ka buga a kasar Afrika ta kudu, dan wasan mai shekarun haihuwa 24 ya zura kwallaye uku in da ya taimakawa Ghana buga wasan dab da kusa dana karshe.

Amma shine kuma ya barrar da bugun da kai sai mai tsaron gida da kasar ta samu a mintin karshe a wasan da ta buga da Uruguay a wasan dab da kusa dana karshe.

Milliyoyin masoya kwallon kafa a duniya, sun ga yadda dan wasan yai ta hawaye bayan da Uruguay ta fidda Ghana a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Duk da koma bayan da dan wasan ya fuskanta a gasar cin kofin duniya, ya bar kungiyar shi ta Rennes a Faransa inda ya kuma Kungiyar Sunderland a Ingila.

"Asamoah dan kwallo ne kwarrrare da ya ke da gaggarumin gudunmuwa a kungiyar Sunderland." In ji Kocin Sunderland Steve Bruce, wanda ya mikawa Gyan kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na BBC.

An fara zaben gwarzon dan kwallon Afrika na BBC na bana ne a ranar 15 a watan Nuwamba, inda aka ba magoya bayan kwallon kafa damar zaben gwarzon na su cikin jerin kasashe 52 a nahiyar Afrika.

An dai dakatar da kada kuri'a ne a ranar 10 ga watan Disamba 2010 a shafin intanet bbc.com/africanfootball da kuma sakon wayar salula.