Gasar zakarun Turai: Arsenal za ta kara da Barca

Gasar zakarun Turai: Arsenal za ta kara da Barca
Image caption Lionel Messi ya zira kwallaye uku a ragar Arsenal a karawar da suka yi abra

Arsenal za ta kara da Barcelona a zagaye na biyu na gasar zakarun Turai. Sai Manchester United da za ta fafata da Marseille.

Yayin da mai rike da kanbun Inter Milan za ta kara da Bayern Munich a wani maimaici na wasan karshen da aka kara a gasar ta bara, inda Inter Milan ta doke Bayern da ci 2-0.

Real Madrid wacce ta lashe kofin sau tara a baya, za ta kara da Olympic Lyon na Faransa.A bara dai Lyon ce ta fitar da Real Madrid a irin wannan zagaye.

Za a buga wadannan wasannin tsakanin ranakun 15-16 da 22-23 na watan Fabreru da 8-9 da 15-16 na watan Maris na shekara ta 2011.

Ga dai yadda rabon kungiyoyin ya kaya:

Roma da Shakhtar Donetsk Milan da Tottenham Valencia da Schalke Inter da Bayern Munich Lyon da Real Madrid Arsenal da Barcelona Marseille da Manchester United Copenhagen da Chelsea