Lampard zai taka leda a wasan da Chelsea za ta buga Man U

Image caption Frank Lampard

Dan wasan Chelsea, Frank Lampard zai fara taka leda a karo na farko tun bayan watan August da ya samu rauni.

Lampard zai taka leda ne a wasan da Chelsea za ta buga da Manchester United ranar lahadi a filin Stamford Bridge.

Dan wasan daya dan jima ya fama da rauni, ya buga wasan horon ne na tsawon minti 60 a ranar alhamis.

Lampard, mai shekarun haihuwa 32, ya dan shafa leda na wasu 'yan mintuna a a wasan da kungiyar Chelsea ta buga da Tottenham a ranar lahadin da ta gabata.

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce Lampard zai fara wasa a wasan da kungiyar za ta buga United saboda ya gama murmurewa.