Inter Milan ta doke TP Mezembe daci uku da nema

etoo
Image caption Etoo ya zira kwallaye 19 cikin karawa 23 da yayiwa Inter

Kungiyar Inter Milan karkashin jagorancin Rafael Benitez ta samu kofinta na farko bayan ta doke kungiyar TP Mezembe ta Kongo a gasar cin kofin zakarun nahiyoyi a birnin Abu Dhabi.

Goran Pandev da Samuel Eto'o da kuma Joseph Biabiany ne suka ciwa Inter kwallaye ukun.

Mazembe ta kafa tarihi a matsayin kungiya ta farko a nahiyar Afrika data kai wannan matakin bayan ta samu galaba akan Internacional ta Brazil a zagayen kusada karshe.

Wannan nasarar da Inter ta samu ya zamo kari a cikin nasarorin data samu na zakarun Turai da Copa Italiya da kuma gasar serie A.