Dusar kankara ta hana gasar premier ta Ingila

premier
Image caption Tambarin gasar premier

Dusar kankara ta tilasta dage wasannin gasar premier ta Ingila daya kamata a buga ranar Lahadi.

Wannan yanayin ya shafi karawa tsakanin Chelsea da Manchester United da kuma na West Bromwich tsakaninta da Wolverhampton sai kuma na Blackpool da Tottenham Hotspur.

Haka zalika bayan tattaunawa da mahukunta a ranar Asabar ma ba a taka leda a wasu daga cikin wasanni hadda na Wigan,Birmingham, Arsenal da ma Liverpool saboda rashin yanayi me kyau.

A nan gaba za a sanarda ranar da za ayi fafatawar, amma dai wadanda suka sayi tikiti zasu iya amfani da shi anan gaba.