Samuel Etoo ne gwarzon dan kwallon Afrika na bana

etoo
Image caption Eto'o shine gwarzon Afrika sau hudu

Kaptin din Indomitable Lions na Kamaru Samuel Etoo Fils wanda ke taka leda a Inter Milan ya samu kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na bana.

An bashi kambunne ne bayan ya samu kuri'u mafi rinjaye akan na Didier Drogba na Ivory Coast da kuma Asamoah Gyan na Ghana.

Wannan kambum da aka baiwa Etoo ya nuna cewar ya kafa sabon tarihi a fagen tamaulan Afrika saboda ya samu wannan kyuatar sau hudu kenan saboda a baya ya samu a shekara 2003 da 2004 da 2005.

Perpetua Nkwocha ta Najeriya ce ta samu kyautar gwarzon 'yar kwallon matan Afrika ta bana sai Ahmed Hassan na Masar daya samu kyautar gwarzon 'yan kwallon cikin gida a yayinda kungiyar TP Mezembe ta samu kyautar kungiyar mafi bajinta a Afrika.

Tawagar Falcons ta Najeriya da Black Stars na Ghana da suka samu kyauta saboda wakilci nagari da suka yiwa Afrika a idon duniya.

Milovan Rajevac wato tsohon kocin Ghana shine ya samu kyautar koci mafi dabara a nahiyar afrika.