Tashin hankali a Congo bayan da Mazembe ta sha kashi a hannu Inter

Image caption Masoya kwallon kafa a birnin Lumbashi a Congo

A Congo, 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masoya kwallon kafa da su ka fito zanga-zanga a birnin Lubumbashi bayan da Inter Milan ta doke TP Mazembe a wasan karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyoyi.

Rahotanni sun bayyana cewa masoya kwallon kafa da ba su ji dadin yadda wasan ta kasance ba, sun shiga gari su na fashe-fashen abubuwa da kone-kone a tituna domin nuna fushin su kan yadda wasan ta kasance.

Inter Milan dai ta doke Mazembe ne da ci uku da nema a wasan karshe a gasar da aka buga a birnin Dubai, da ke hadadiyar daular larabawa.

Masoya kwallon kafan kasar dai sun fusata ne, saboda sun zargi alkalin wasan da rashin nuna adalci.