Carlos Tevez ya yi amai ya lashe akan Manchester City

Tevez
Image caption Carlos Tevez ya maida wukar

Kungiyar Manchester City ta ce dan kwallonta Carlos Tevez ya janye bukatarshi na barinta.

Tevez a farkon wannan watan ya bayyana cewar yanason ya bar City saboda rashin jituwarshi da mahukunta kungiyar.

Amma dai a wata sanarwa da City ta fitar a yau litinin ta ce dan kwallon Argentina din a yanzu ya maida wukar kuma ya jaddada biyyarshi da sadaukarwarshi ga cigaban kungiyar.

Sanarwar ya kara da cewar an warware komai akan batun kuma yarjejeniyar Tevez babu canji akai sannan da Tevez din da kungiyar duk zasu maida hankali ne akan abinda ke gabansu.