Manchester City ta sha kashi a hannun Everton

Image caption 'Yan wasan Everton na murnar zura kwallo

Duk da cewa Carlos Tevez ya taka leda a wasan da City ta karbi bakonci Everton, dan wasan ya kasa taimakawa kungiyar, inda ta sha kashi a hannun Everton da ci biyu da daya.

Tevez wanda ya yi amai ya lashe a yinkurinsa na barin kungiyar bai taka rawar gani ba.

Tim Cahill da Leighton Baines ne suka zurawa Everton kwallayen ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci, sannan kuma da aka dawo an sallami Victor Anichebe.

Yaya Toure ya fanshewa City kwallo guda, kafin kuma aka sallami Kolo Toure bayan an kusan kammala wasan.