Ghana za ta nada kocin Black Stars a karshen wata

kwesi
Image caption Kwesi da jami'an GFA na jan kafa akan nada koci

Daga nan zuwa karshen shekara ne Ghana za ta nada sabon mai horadda 'yan kwallonta don maye gurbin Milovan Rajevac wanda ya bar Black Stars a watan Satumbar data wuce.

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Ghana GFA ta riga ta yiwa mutane uku jarabawa akan mukamin don samun wanda yafi dacewa yaja ragamar tawagar 'yan kwallon kasar.

Shugaban GFA Kwesi Nyantakyi ya bayyana cewar "shirye shirye na tafiya lami lafiya kuma muna saran zamu bada sanarwa a karshen wata"

Mutane ukun dake neman kocin Black Stars dai sune tsohon kocin Portugal Humberto Coelho da dan Serbia Goran Stevanovic sai dan Ghana Herbert Addo a yayinda Marcel Desailly ya janye daga neman mukamin.

Coelho wanda a baya ya jagoranci Morocco da Tunisia da kuma Koriya ta Kudu ya gana da jami'an GFA a makon daya gabata kuma ya ce sun samu tattaunawa mai ma'ana.