Messi zai kara da Ronaldo a filin Emirates

messi da ronaldo
Image caption Lionel Messi da Christaino Ronaldo zarata ne

Argentina da Portugal zasu buga wasan sada zumunci a filin Arsenal na Emirates a ranar tara ga watan Fabarairu.

Wasan sada zumuncin zai hada wasu daga cikin zaratan 'yan kwallo a duniya wato dan Argentina Lionel Messi da dan Portugal Cristiano Ronaldo.

Wasan zai zamo kusan fafatawa biyu a jere da Messi zai yi a London gannin cewar a ranar 16 ga watan Fabarairu Arsenal za ta dauki bakuncin Barcelona.

A baya kasashen biyu duk sun taba taka leda a filin Emirates inda Argentina ta sha kashi a wajen Brazil daci uku da nema a shekara ta 2006 a yayinda ita kuma Portugal ta doke Brazil daci biyu da nema a 2007.

Baya ga Messi da Ronaldo wasu daga cikin shahararrun 'yan kwallon da zasu buga wasan sune dan Manchester City Carlos Tevez da Javier Mascherano na Barcelona duk a bagaren Argentina, sai Jose Bosingwa, Nani, Ricardo Carvalho da Raul Meireles a Portugal.