Robben zai dawo tamaula a watan Junairu-Van Gaal

robben
Image caption Robben ya haskakawa Holland a Afrika ta Kudu

Kocin Bayern Munich Louis van Gaal ya bayyana cewar dan kwallonshi Arjen Robben zai koma taka leda a gasar Bundesliga tsakaninsu da Wolfsburg a ranar 15 ga watan Junairu.

Dan kwallon Holland din bai taka leda ba tun bayan kamalla gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu saboda rauni a kafadarshi.

Van Gaal yace "ya fara horo kuma baya cikin damuwa".

Robben zai buga wasan sada zumunci a ranar 12 ga watan Junairu sannan kuma sai bayan kwanaki uku ya fafata da Wolfsburg akalla na minti talatin.

Amma dai van Gaal ya ce dan kwallon me shekaru 26 wasansu na ranar Laraba tsakaninsu da Stuttgart.