Za a nada David Bernstein a matsayin shugaban FA na Ingila

David Bernstein
Image caption David Bernstein zai zama shugaban FA a nan gaba

An bada sunan tsohon shugaban kungiyar Manchester City David Bernstein don zamowa sabon shugaban hukumar kwallon kafan Ingila wato FA.

Bernstein me shekaru sittin da bakwai ya shafe shekaru tara a kwamitin gudanarwar City sannan shekaru biyar a matsayin shugaba.

Daukacin mambobin hukumar FA sun amince da a mika sunan Bernstein a taronsu na ranar Laraba sannan majalisar kolin FA zata amince da nadin a ranar 25 ga watan Junairun badi.

Bernstein yace "naji dadin wannan sabon matsayin na shugaban FA".

A shekaru taran daya shafe a Manchester City ya maida kungiyar gasar premier sannan ya jagoranci sasantawa akan samun sabon filin wasansu na Eastlands.

Bernstein ya yi murbus ne a matsayin shugaban City a shekara ta 2003 bayin rashin jituwa tsakaninshi da kocin kungiyar Kevin Keegan akan batun sayen Robbie Fowler.