Ba ni nafi kowa a Afrika ba - Eto'o

Ba ni nafi kowa a Afrika ba - Eto'o
Image caption Eto'o ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika a karo na hudu.

Dan Kamaru Samuel Eto'o ya nesanta kansa da kalaman da ake yi cewa shi ne yafi kowanne dan wasa a tarihin kwallon Afrika, duk da ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika a karo na hudu.

Dan wasan na Inter Milan mai shekaru 29, ya lashe kyautar ne bayan nasarorin da ya samu da kungiyar a bana.

A yanzu dan wasan ya lashe kyaututtuka da kuma kofuna fiye da kowanne dan wasa a nahiyar Afrika.

"Ba na zaton lashe kyautar sau hudu ya isa ace nine nafi kowa iya kwallo a Afrika," a cewar dan wasan.

Ya kara da cewa: "Akwai kwararrun 'yan wasa da aka yi a baya, kuma sun fuskanci kalubale da dama idan aka kwatanta da ni. Ba za ka iya hada lokaci na da na su ba.