Ana takaddama akan daukar nauyin gasar premier ta Najeriya

Maigari
Image caption Shugaban NFF Aminu Maigari yana kalubantar NPL

Batun kamfanin da zai dauki nauyin gasar premier ta Najeriya ya janyo sa-in-sa tsakanin hukumar NFF da hukumar NPL mai kula da gasar a kasar.

Hukumar NPL ta kulla yarjejeniya ta shekaru hudu akan dala miliyan 17 da kamfanin sadarwa ta MTN amma sai NFF ta ce hakan ba zai yiwu ba.

Kakakin NFF Ademola Olajire ya shaidawa BBC cewar wannan yarjejeniyar zata saka gasar kasar cikin mawuyacin hali.

Yace"hukuncin da NFF ta dauka ya sabawa ka'idojin kwallon kafa a kasar".

Shugaban NPL Davidson Owumi wanda a yanzu haka ake kalubantar zabenshi gaban kuliya ya ce hukumarsu tayi abinda ya dace game da yarjejeniyar.