Inter Milan ta kori Rafael Benitez

Benitez
Image caption Al'amura ba sa tafiya daidai a Inter tun lokacin da Benitez ya karbi ragama

Inter Milan ta kori Rafael Benitez a matsayin kocinta, bayanda dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da shugabannin kungiyar.

Hakan na zuwa ne bayanda ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar zakarun nahiyoyin duniya a ranar Asabar, sai dai suna mataki na bakwai a gasar Serie A wacce suka lashe a shekaru biyar din da suka wuce.

Rahotanni daga Italiya sun ce an cimma matsaya tsakanin kocin da kuma jami'an Inter Milan, bayan tattaunawar da bangarorin biyu suka yi.

Tun da farko Benitez ya musanta cewa an kore shi, bayanda wasu rahotanni suka bayyana hakan.

Dangantaka ta yi tsami ne tsakanin Benitez da Inter, bayanda kocin ya nemi kulob din ya kore shi ko kuma a kyale shi sakamakon nasarar da ya yi a gasar cin kofin nahiyoyin duniya.