Edwin Van der Sar zai yi ritaya badi

Van der saar
Image caption Edwin van der Sar na shirin yin ritaya

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce golansu Edwin van der Sar na Holland zai yi ritaya a karshen kakar wasa ta bana.

Ferguson ya ce United na shirin samun wanda zai maye gurbin van der Sar a cikin fili, duk da cewar za a iya rikeshi a matsayin koci a Old Trafford.

Yace"muna shiri akan tafiyarshi a karshen kakar wasa ta bana".

A makon daya gabata ne United ta tabbatar da samun Anders Lindegaard daga kungiyar Aalesunds FK a yarjejeniya ta shekaru uku da rabi.

Golan mai shekaru ashirin da shida ya fara horo tare da United kuma a watan Junairu za ayi mashi rijista sannan a gabatar dashi gaban 'yan kallo.