Kamfanin MTN zai dauki nauyin gasar premier ta Najeriya har zuwa 2014

maigari
Image caption Shugaban NFF Aminu Maigari

Bayan shafe makwanni ana buga gasar premier ta Najeriya ba tare da kamfannin da zai dauki nauyin gasar ba,a yanzu haka dai an warware takkada akan batun bayan sa-in sa da aka yita yi akan baiwa kamfanin MTN damar daukar nauyin gasar.

Hakan dai ya kawo karshen yarjejeniya da kamfanin GLO wanda ya kwana biyu yana daukar nauyin gasar.

A bisa tsarin dai hukumar dake kula da gasar premeir ta Najeriya wato NPL zata karbi dala miliyan 17 daga wajen MTN don daukar nauyin gasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

A ranar laraba ne hukumar wasanni kasar ta baiwa hukumar NPL din damar sanya hannu a yarjejeniya tsakaninta da kamfannin sadarwar kamar yadda mataimakin shugaban NPL Alhaji Shehu Gusau ya sanar.

Wannan na nufin cewar daga mako mai zuwa kamfanin sadarwa na MTN shine zai kasance uwa ga gasar premier ta Najeriya.