FIFA ta nada kwamitin zabe a Kenya

Leodegar Tenga
Image caption Leodegar Tenga Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Gabashin Afrika

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta nada kwamitin mutane 8 domin ya shirya zabe a Hukumar kwallon kafa ta Kenya a watan Aprilun badi.

Daga cikin wadanda suka samu shiga kwamitin akwai tsohon dan kwallon kasar Joe Masiga da kuma Nahashon "Lule" Oluoch.

Leodegar Tenga, wanda shi ne shugaban Hukumar kwallon yankin Gabashin Afrika Cecafa, shi ya bada sanarwar a wani taron manema labarai a birnin Nairobi. "Babban aikin kwamitin shi ne na shirya zabe mai inganci," a cewar Tenga, wanda shi ne shugaban Hukumar kwallon kafa ta Tanzania.

Joe Okwach, wanda lauya ne daga kasar ta Kenya, shi ne zai shugabanci kwamitin zaben mai zaman kansa.

Wannan mataki da FIFA ta dauka, ya biyo bayan rigimar da aka dade ana yi ne a Hukumar Kwallon ta Kenya.