Mancini ya gargadi Mario Balotelli

Mario Balotelli
Image caption Mario Balotelli yana da kwarewa sosai, amma akwai rashin da'a

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce wajibi ne Mario Balotelli ya dage domin kare matsayinsa na matashin dan wasan da ya fi kowanne a duniya.

Bayanda ya lashe kyautar ta Hukumar FIFA, Balotelli ya ce bai san da dan wasan Arsenal Jack Wilshere wanda ya zo na biyu ba, sannan ya ce kusan daidai yake da Lionel Messi.

Sai dai kociyansa Mancini ya ce dole ne ya bi kalaman nasa da aiki na zahiri - sannan ya gyara halinsa.

"Idan kana taka leda a kowanne wasa ne kawai za ka fadi haka," a cewar Mancini. "Akwai bukatar ka saki ranka yayin da kake buga kwallo."

Balotelli ya taka rawar gani tun bayan zuwansa City daga Inter Milan, amma an ba shi jan kati sakamakon rashin da'ar da ya nuna.