Man United za ta kara da Barca

Man United za ta kara da Barcelona
Image caption Barca ce ta doke United da ci 2-0 a wasan karshe da suka buga

Manchester United za ta fafata da Barcelona a wasan sada zumunta da za su kara a birnin Washington na kasar Amurka.

Kamar yadda sanarwar da shafin intanet na Barcelona ya fitar, za a buga wasan ne a ranar 30 ga watan Yulin 2011.

Duk da cewa United ba ta tabbatar da shirye-shiryenta na hutun kakar bana ba, ana saran za ta ziyarci Amurka a wannan karon ma.

Karawar karshe da kungiyoyin biyu su ka yi dai, ita ce ta wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai, inda Barca ta doke United da ci 2-0.