'Rafali ne ya ci mu' - Ferguson

Alex Ferguson
Image caption Alex Ferguson

Majan kulob din Manchester United Sir Alex Ferguson ya soki rafali Lee Mason saboda rashin soke cin da kulob din Birmingham suka yi wa kulob dinsa a 'yan mintunan karshe na wasan da suka tashi daya da daya.

Ferguson ya ce kwallon ta taba hannun dan wasan Birmingham kuma an yi wa Rio Ferdinand keta kafin a ci kwallon, amma rafali ya kau da kai.

" Shi ya sa muka ce wa hukumomin gasar Premier su nemo rafali da zai iya ganin irin wadannan laifuka da 'yan wasa suke aikata wa a filin wasa." In ji Ferguson.

Kulob din na Manchester dai da farko yana gaban Birmingham da da ci dayan da Dmitar berbatov ya jefa masa, kafin daga bisani ana sauran 'yan mintuna a kare wasan Lee Bowyer na kulob din Birmingham ya farke.