Tottenham na jira a saki David Beckham

Beckham
Image caption watakila angulu ta koma gidanta na tsamiya

Tottenham na daga cikin kulab-kulab din Premier dake dakon ganin ko Los Angeles Galaxy zai ba da aron tsohon kaftin din Burtaniya, David Beckham a watan da muke ciki.

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya ce dan wasan, dan shekaru 35 na son shiga Spurs, kuma kulob din Newcastle da Blackburn suma suna sha'awar ganin ya amince da tayinsu.

Harry Redknapp zai yi kokarin kawo tsohon kyaptin din Ingila David Beckham zuwa White Hart Lane a matsayin aro daga LA Galaxy a watan Janairu.

Za a koma gasar kwallon Amurka wato Major league ne a ranar 15 ga watan Maris abinda zai iya baiwa Redknapp damar kulla yarjejeniyar wucin gadi da dan kwallon mai shekaru 35.

Redknapp yace"Za mu tuntubi LA Galaxy idan zasu barshi ya zo na watanni uku, idan suka yarda zamu kulla yarjejeniya".

Beckham a baya ya taba kulla irin wannan yarjejeniyar da kungiyar AC Milan ta Italiya a 2009 da 2010.

Tsohon dan kwallon Manchester United da Real Madrid din dai an haife shi a arewacin London kuma ya yi horo da Tottenham kafin kulla yarjejeniya da Red Devils. Beckham a watan Nuwamba ya ki amince da bukatar Everton na daukar shi na wucin gadi sannan kungiyoyin West Ham da Leicester sun nuna sha'awarsu amma yaki yarda.