Ba zan sayi sabbin 'yan kwallo ba -Ferguson

ferguson
Image caption Sir Alex Ferguson ya bada aron 'yan kwallo uku

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce ba zai sayi sabbin 'yan kwallo ba a watan Junairu idan an bude kasuwar musayar 'yan kwallo.

A lokacin da aka tambayeshi ko zai saye sabbin 'yan kwallo, sai Ferguson yace "tabbas babu sabbin 'yan wasa".

Sai dai ana saran Ferguson zai bada aron Federico Macheda har zuwa karshen kakar wasa ta bana don dan kwallon ya kara gogewa.

Dan kwallon me shekaru goma sha tara ya bugawa United wasa a karawa bakwai a kakar wasa na bana kuma ana tunanin zai koma Lazio ko Roma ko Bolton.

Ferguson ya kuma tabbatar da cewar Danny Welbeck da Mame Biram Diouf zasu cigaba da kasancewa a kungiyoyin Sunderland da Blackburn na wucin gadi.