Shugaban hukumar kwallon kafan Benin ya dawo kan aiki

Image caption Anjorin Moucharafou

Mahukunta a kasar Benin sun dawo da shugaban hukumar kwallon kasar Anjorin Moucharafou kan kujerarshi domin gujewa fushin hukumar kwallon kafa na duniya wato FIFA.

Hukumar FIFA dai tayi barazanar dakatar da kasar muddin bata dawo da Moucharafou kan kujerarshi ba.

Ma'ikatar kula da wasanni ta Benin ta yi amfani da karfin tuwo wajen tsige Moucharafou saboda rikicin shugabanci a hukumar kula da kwallon kafan kasar.

"Ma'ikatar kula da wasanni ta rubutomin cewa da in dawo kan kujera ne a ranar litinin, kuma ta ce ba za ta tsoma baki cikin aiki na ba," Moucharafou a hirarsa da BBC.