Mido ya fice da Ajax Amsterdam

Mido
Image caption Wasu kungiyoyi a Spain da Ingila na zawarcin Mido

Dan kwallon gaban Masar Ahmed Mido Hossam ya bar kungiyar Ajax Amsterdam watanni biyar da zuwanshi.

Dan shekaru ashirin da bakwai da haihuwa ya ce mahukunta kungiyar sun amince da bukatarshi na barinsu.

Mido ya koma Ajax ne a watan Satumba a yarjejeniya ta wucin gadi ta shekara guda a karkashin jagorancin Martin Jol.

Amma Jol ya ajiye mukaminshi kuma an maye gurbinshi da Franck de Boer a matsayin koci abinda ya tilastawa dan Masar din ya tafi.

Mido yace"ta kare, na amince da mahukunta Ajax na sauya yarjejeniyar".

A baya Mido ya taka leda a Ajax daga 2001 zuwa 2003.

Ya kara da cewar wasu kungiyoyi daga Spain da Ingila sun nuna muradin sayenshi.

Mido ya taka leda a kungiyoyi goma daban daban tun daga Zamalek zuwa Marseille da Celta Vigo da Roma da West Ham.