Blackburn ta taya Ronaldinho akan pan miliyan 20

ronaldinho
Image caption Ronaldinho 'na da sha'awar gasar premier'

Kungiyar Blackburn Rovers ta Ingila ta bada tayin pan miliyan ashirin akan dan kwallon AC Milan Ronaldinho don ya taka mata leda na shekaru uku.

Venky's, kamfanin daya sayi Rovers a shekara ta 2010, ya ce ofishinshi na Brazil na tattaunawa da wakilin dan kwallon mai shekaru talatin da haihuwa.

Shugabar Venky's Anuradha Desai ta shaidawa BBC cewar "dan kwallon nada muradin taka leda a gasar premiership".

Desai ta kara bayyana cewar Rovers na kokarin sayen David Beckham na wucin gadi daga kungiyar Los Angeles Galaxy ta Amurka.

A cewarta kungiyar ta shirya sayenshi duk lokacin da yake so.

Beckham a kwannan nan ya shiga cikin batun jita jita akan makomarshi saboda kungiyoyin gasar premiership da dama suna zawarcinshi.