U 20: Ghana za ta hadu da Najeriya da Kamaru

Ghana
Image caption Ghana ce ta lashe gasar da aka gudanar a 2009

Mai rike da kofin gasar cin kofin kwallon Afrika na 'yan kasada shekaru 20 wato Ghana za ta Najeriya da Kamaru da Gambia a rukuni guda a gasar da za a fara a watan Maris.

Mai masaukin baki Libya na daya rukunin tare da Mali da Masar da kuma Lesotho.

Za a fara gasar ce daga ranar 18 ga watan Maris zuwa daya ga watan Afrilu, kuma kasashe hudu da suka kai zagayen kusada karshe zasu wakilci Afrika a gasar duniya a badi.

Har wa yau Ghana itace ta lashe gasar kofin duniya kuma ta shirya kare duka kofinan.