Ben Arfa ya kulla yarjejeniya da Newcastle

ben arfa
Image caption Hatem Ben Arfa na murnar zira kwallo

Newcastle United ta kamalla kulla yarjejeniya da dan kwallon Faransa Hatem Ben Arfa daga Marseille akan kudin da ba'asan yawansu ba.

Dan shekaru ashirin da ukun ya sanya hannu a kwangilar da zata sa ya tsaya a St James Park har zuwa watan Yunin 2015, bayan ya shafe watanni hudu na wucin gadi a kungiyar.

Ben Arfa yace"na yi matukar jin dadin kulla yarjejeniya da Newcastle United na dindin din".

A yinkurin kara karfin kungiyar sabon kocin Newcastle Alan Pardew ya sanarda cewar Steven Taylor ya sabunta yarjejeniyarshi.