Man United ta yi galaba akan Stoke

Image caption Nani ne ya zura kwallon da ya ba Man U nasara

Manchester United ta kara tazarar maki uku tsakaninta da Manchester City a gasar Premier ta Ingila bayan ta yi nasara a kan Stoke City da ci biyu da guda.

Javier Hernandez ne ya zurawa Manchester United kwallonta na farko kafin a tafi hutun rabin lokaci, sannan Dean Whitehead ya fanshewa Stoke bayan an dawo.

Nani ne dai ya zura kwallon da ya ba Manchester United nasara a wasan.

Ba'a dai doke Manchester United a wasa ko guda ba gasar Premier ta bana.