Arsenal ta buga canjaras da Man City

Arsenal ta buga canjaras da Man City
Image caption Robin van Persie da Cesc Fabregas da Theo Walcott sun barar da damarmaki masu yawa

Arsenal da Manchester City sun zubar da damar matsa lamba ga Manchester United bayanda suka tashi canjaras a wasan da suka fafata a filin wasa na Emirates.

Duka kungiyoyin biyu sun zubar da damarmaki da yawa, abinda yasa Manchester United wacce ke kan gaba a tebur ta kara yi musu tazara.

Arsenal wacce ke mataki na uku, ita ta mamaye wasan, inda Robin van Persie da Cesc Fabregas da Theo Walcott suka barar da damarmaki masu yawan gaske.

Walcott ya yi zargin ya samu bugun fanareti amma alkalin wasa ya hana shi.

Daga bisani alkalin wasan ya kori Bacary Sagna na Arsenal da Pablo Zabaleta na Manchester City bayanda suka barke da fada.