U 17:Rwanda ta shirya daukar bakuncin Afrika

caf
Image caption Najeriya da Ghana basu tsallake buga gasar ba

Rwanda na shirye shiryen daukar bakuncin gasar cin kofin Afrika ta 'yan kasada shekaru 17 a ranar Asabar mai zuwa.

Kasashe hudun da suka tsallake zuwa zagayen kusada karshe zasu wakilci Afrika a gasar cin kofin duniya a Mexico nan gaba a cikin wannan shekarar.

Shugaban kwamitin shirya gasar a Rwanda Emmanuel Bugingo ya ce ya kammala duk abinda ya kamata don samun nasara saboda shekaru biyu da suka wuce sun dauki bakuncin gasar 'yan kasada shekaru 20.

A rukunin farko akwai mai masaukin baki Rwanda tare da Burkina Faso da Senegal da Masar.

A rukuni na biyu akwai Gambia da Congo Brazzaville da Ivory Coast da kuma Mali.

Rwanda ce zata buga wasan farko tsakaninta da Burkina Faso a ranar takwas ga watan Junairu.