Zai yi wuya mu lashe gasar Premier-Ancelotti

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti
Image caption Ancelotti yana cikin tsaka mai wuya

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce zai yi wuya kungiyar ta lashe gasar Premier ta bana, bayanda suka sha kashi a hannun Wolves da ci daya mai ban haushi.

Kwallon da Jose Boswinga ya zira a ragar kungiyarsa a minti na biyar da fara wasan, ta sa Chelsea kasance wa a mataki na biyar a tebur, inda Manchester United ta bata tazarar maki tara.

Ancelotti ya ce: "zai yi wuya mu lashe gasar, amma abu mai mahimmanci shi ne mu ci gaba da samun nasara."

Ya kara da cewa yana "cikin matsin lamba" amma ba ya tunanin zai rasa aikinsa.

An fara matsawa kocin lamba ne tun bayanda kungiyar ta fara samun koma baya a gasar ta Premier a watan Oktoba.