Kenny Dalgish ya maye gurbin Hodgson a Liverpool

dalgish
Image caption Kenny Dalgish tsohon dan Liverpool ne

Kenny Dalglish ya koma jan ragamar Liverpool a wasanta na farko inda ta sha kashi a wajen Manchester United daci daya me ban haushi a wasan gasar cin kofin FA a filin Old Trafford.

Tsohon dan kwallon Liverpool Dalglish me shekaru 59 zai ja ragamar kungiyar har zuwa karshen kakar wasa ta bana sakamakon murabus din da Roy Hodgson ya yi.

Kalubalen dake gaban sabon kocin shine kokarin kai Liverpool zuwa mataki na sama sama akan teburin gasar premier ganin cewar itace ta 12 a halin yanzu.

Dalgish ya nuna rashin jin dadinsa da tafiyar Hodgson amma ya ce zai kokarta don maido da martabar kungiyar.