Liverpool ta nada Steve Clarke mai horadda 'yan kwallonta

clarke
Image caption Sabon mai horadda Liverpool Steve Clarke

Liverpool ta nada tsohon dan kwallon Chelsea da West Ham Steve Clarke a matsayin mai horadda 'yan kwallonta.

Clarke me shekaru 47 an nadashi ne a tsarin garan bawul da Liverpool ta soma tun bayan baiwa Kenny Dalglish manajan 'yan kwallonta sakamakon ficewar Roy Hodgson a ranar Asabar.

Dalglish yace:"Steve babban kari ne a cikin tawagarmu kuma naji dadin kawo shi".

Clarke ya halarci sansannin horon Liverpool dake Melwood a ranar Litinin, kuma ya buga wasanni fiye da 500 a St Mirren da Chelsea, kuma ya taba kasancewa mataimakin manajan Newcastle United.

Ya bar West Ham ne a kashin kanshi a watan Yunin 2010 bayan korar Gianfranco Zola.