Ingila za ta kara da Ghana a wasan sada zumunci

capello
Image caption Kocin Ingila Fabio Capello

Ingila za ta buga wasan sada zumunci tsakaninta da Ghana a watan Maris mai zuwa.

Amma dai Ingilar ta janye daga wasan data shirya bugawa da Thailand.

Ingilan zata kara da Ghana ne a karon farko a filin wasa na Wembley a ranar 29 ga watan Maris, kwanaki uku bayan ta fafata da Wales a wasan neman gurbin gasar cin kofin kasashen Turai a 2012.

A gasar cin kofin duniya da aka buga a Afrika ta Kudu a bara, Ghana ta kai zagayen gabda na kusada karshe.

Hukumar dake kula da kwallon Ingila FA ta bayyana cewar amma kwamitin gudanarwatta bata amince da fafatawarsu da Thailand ba.