An nada Paul Jewell a matsayin manajan Ipswich Town

ipswich
Image caption Paul Jewell na Ipswich

An nada Paul Jewell a matsayin sabon manajan Ipswich Town.

Jewell ya kulla yarjejeniya ta shekaru biyu da rabi da Ipswich din, kuma tun Disamban 2008 bai da aikin yi bayan yayi murabus a kungiyar Derby.

Jewell ya ce "na ji dadi matuka saboda shekaru biyu ban shiga wasa ba".

Sabon manajan Ipswich din mai shekaru 46 ya maye gurbin Roy Keane a Portman Road.

An kori Keane a ranar Juma'a bayan kungiyar ta sha kashi a wasanni bakwai cikin tara.