Messi ne gwarzon dan kwallon duniya na 2010

messi
Image caption Lionel Messi ya samu kyautar sau biyu kenan

Lionel Messi na Argentina ya samu kyautar gwarzon dan kwallon duniya na 2010.

Ya samu kyautar ce bayan ya doke takwarorinshi na Barca wato Andres Iniesta da Xavi Hernandez.

A bana Fifa ta hada kai da mujallar Faransa wacce ke bada kyautar gwarzon dan kwallon Turai inda kyautar ta zama 'Fifa Ballon d or'.

Lionel Messi na Argentina shine ya samu wanna kyautar wato sau biyu kenan a jere saboda irin rawar daya taka a matsayinshi na dan kwallon Barcelona duk da cewar bai haskaka ba a matsayinshi na dan kwallon Argentina a gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

A bangaren mata kuwa 'yar Brazil Marta ce aka baiwa kyautar mace mafi bajinta a fagen tamaula a bara.

Har wa yau a daren jiyan, Fifa ta sanarda 'yan kwallon 11 a matasyin tawaga daya, wanda sune son kowa kin wanda ya rasa. Kuma gola shine Ike Casilas na Real Madrid sai a baya akwai Maicon da Lucio da Gerrard Pique da kuma Carlos Puyol. 'Yan tsakiya kuwa sune Wesley Schnieder da Xavi Hernandez da Andres Iniesta a yayinda 'yan gaba aka zabo Lionel Messi da David Villa da kuma Christiano Ronaldo.

Fifa har ila yau ta bullo da sabon kyauta wato na mai horadda 'yan kwallo mafi kwarewa inda Jose Mourinho na Real Madrid da Vicente Del bosque na Spain da kuma Pep Guardiola na Barcelona suka yi takara inda daga karshe the special one ya samu.

Hamit Altinop na Turkiya shine ya samu kyautar zira kwallon da yafi kowanne sarkakiya a bara.