Ronaldo ya taimakawa Madrid a wasanta da Villareal

Image caption Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye uku a wasan da Real Madrid ta lallasa Villarreal da ci 4-2 a filin Bernabeu.

Kaka shima dai ya zura kwallon shi na farko a wasan a kakar wasan bana, bayan ya yi ta fama da rauni.

Villarreal ta shiga gaban Madrid sau biyu a wasan inda Cani da Marco Ruben su ka zura kwallaye, amma dai duk Cristiano Ronaldo ne ya fashe Madrid kwallayen kafin kuma ya zura ta uku.

Kaka ne ya zura ta hudun bayan ya shigo daga kan benci.

A yanzu haka dai Madrid na bayan Barcelona ne wadda ke jagoranci a gasar lalliga da maki biyu.