Thierry Henry ya soma horo a Arsenal

henry
Image caption Henry ya taimakawa Faransa da hannu

Tsohon kaptin din Arsenal Thierry Henry ya soma horo tare da tsohuwar kungiyarshi don ya kasance cikin koshin lafiya sakamakon hutun da ake yi a gasar kwallon Amurka.

Dan kwallon Faransan mai taka leda a New York Red Bulls a ranar Litinin ne ya koma filin horo a gunners.

Henry ya kasance mai farin jini a tsakanin magoya bayan Arsenal bayan ya kafa tarihi inda ya zira kwallaye 226 cikin wasanni 370 da ya buga daga 1999 zuwa 2007.

Dan kwallon mai shekaru 33 ya bar Arsenal ya koma Barcelona a shekara ta 2007 kafin ya kulla yarjejeniya da New York a bara.

Sanarwa daga Arsenal ta ce "Thierry Henry ya dawo Arsenal".