Ghana ta nada Goran Stevanovic a matsayin koci

stevanovic
Image caption Sabon kocin Ghana Goran Stevanovic

Ghana ta kulla yar jejeniya da dan Serbia Goran Stevanovic a matsayin sabon kocin 'yan kwallon Black Stars don maye gurbin Milovan Rajevac wanda ya jagoranci kasar zuwa gasar cin kofin duniya a bara.

Sanarwar da hukumar kwallon Ghana GFA ta fitar ta ce a ranar Litinin ta ce an kamalla duk mai yiwuwa tsakanin Ghana da sabon kocin mai shekaru 44.

Tsohon kocin Partizan Belgrade Stevanovic a ranar Laraba ne ake saran za a gabatar dashi a bainar jama'a a birninn Accra.

Wasanshi na farko a matsayin kocin Black Stars shine wanda zai jagoranci kasar a karawatta da Congo a birnin Brazzaville na neman cancantar buga gasar cin kofin kasashen Afrika a 2012.