Ronaldinho ya koma Flamengo

Image caption Ronaldinho

Dan wasan Brazil da ke takawa AC Milan leda Ronaldinho ya koma kungiyar Flamengo dake birnin Rio de Janeiro a kasar.

Komarwar tasa ya kawarda duk wasu rohatannin dake nuni da cewa dan wasan zai koma kungiyar Blackburn dake Ingila.

Dan wasan mai shekaru 30 da haihuwa ya koma AC Milan ne daga kungiyar Barcelona a shekarar dubu biyu da tawas.

Kungiyar Gremio da Palmeiras ma sun nemi su sayi dan wasan, amma bai yiwuba. Ronaldinho dai zai takawa kungiyar leda har zuwa shekarar 2014.