Ballon d'Or:Jaridun Spain sun soki Blatter

blatter
Image caption Ana zargin Fifa akan cin hanci da rashawa

Jaridu a kasar Spain sunyi kakkausar suka akan shugaban Fifa Sepp Blatter bayan da Lionel Messi ya doke 'yan Spain biyu Andres Iniesta da Xavi Hernendez a takarar kyautar gwarzon dan kwallon duniya.

Jaridar AS ta ce "Spain na cikin fushi" a yayinda jaridar Marca ta ce "Gwarzaye biyu da mai kin jinin Spain daya", ita kuwa ABC cewa tayi"Fifa ta cuci zakarun kwallon duniya".

Messi ya samu kyautar gwarzon dan kwallon duniya sau biyu kenan a jere inda ya shiga gaban takwarorinshi na Barcelona wato Xavi da Iniesta wadanda suka taimakawa Spain ta lashe gasar cin kofin duniya a karon farko a tarihinta.

Iniesta ne yaci kwallon daya baiwa Spain nasara a wasan karshe tsakaninta da Holland a filin wasa na Soccer City a Johannesburg a yayinda ake ganin cewar Xavi ne kashin bayan nasarar Spain a 'yan shekarunan

Sai dai Fifa ta zabi 'yan kwallon Spain shida cikin tawagar shaharrarrun 'yan kwallo goma sha daya a duniya.