Spain za ta fafata da 'yan kwallon Afrika

iniesta
Image caption Andres Iniesta ne yaci kwallon daya baiwa Spain kofin

Zakarun kwallon duniya Spain zasu fafata da tawagar 'yan kwallo goma sha daya na Afrika a wasan sada zumunci a kasar Afrika ta Kudu.

Ministan wasanni Afrika ta Kudu Fikile Mbalula wanda ya bada sanarwar, ya ce wasan sada zumuncin nada nufin nuna godiya saboda gasar cin kofin duniya da akayi na farko a nahiyar Afrika

Koda yake dai ba a bayyana ainihin ranar da za a buga wasan ba, amma dai a cikin watan Yuni ne wato shekara guda cif da yin gasar data fi kowacce kayatarwa a duniya.

A lokacin gasar cin kofin duniya a bara a Afrika ta Kudu, Spain ce ta lashe gasar bayan ta samu galaba akan Holland daci daya me banhaushi a yayinda Jamus ta zama ta uku.