Balotelli zai shafe wata guda yana jinya

balotelli
Image caption Mario Balotelli

Dan kwallon Manchester City Mario Balotelli ba zai taka leda ba na tsawon wata guda saboda rauni.

Dan shekaru ashirin din dai bai buga wasa dayawa ba a kakar wasa ta bana saboda tiyatar da aka yi mashi a gwiwa.

Kocin City Roberto Mancini ya ce "na damu matuka saboda ba zai buga ba na makwanni a wannan lokacin mai mahimmanci".

Ya kara da cewar abin mamaki ne ayiwa mutum tiyata sannan kuma bayan watanni biyu ciwon ya kara dawowa.

Wannan raunin da dan Italiyan ya kamu dashi na zuwa ne a ranar da aka gabatar da sabon dan kwallon gaban City Edin Dzeko wanda ake ganin zai maye gurbinshi.

Haka zalika raunin Balotelli watakila ya sa a fasa sayarda Emmanuel Adebayor wanda a baya ake tunanin za a sayarda shi.