Hukumar CAF ta hukunta Esperance ta Tunisia

esperance
Image caption Tawagar 'yan kwallon Esperance

Kungiyar Esperance ta Tunisia za ta buga wasanni biyu na gasar cin kofin zakarun Afrika ba tare da 'yan kallo ba sakamakon abubuwan da suka faru a wasan karshe na gasar a bara.

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Afrika Caf wacce ta bada wannan hukuncin ta kuma dage dan kwallon Esperance Aymen Ben Amour daga buga wasanni shida tare da tarar dala dubu goma.

Dan kwallon dai an koreshi lokacin wasan saboda ya tofa yawu ga dan kwallon TP Mezembe.

Har wa yau, an ci tarar Esperance din dala dubu hamsin da biyu da dari biyar saboda laifuka daban daban hadda laifin wurga kwalabe ga manyan baki a lokacin wasan.

Itama dai TP Mezembe an ci tarar ta dala dubu biyar saboda rashin ladabin wasi daga cikin tawagarta a Tunisia.